Mataimakin gwamnan jihar Kano Prof Hafiz Abubakar ya yi murabus

LATEST
Mataimakin gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafiz Abubakar ya yi murabus bayan an shafe watanni ana takun saka tsakaninsa da gwamnan.
Farfesa Hafiz Abubakar
Mataimakin gwamnan ya sanar da murabus din nasa ne a wata wasika da ya mika ma gwamnan jihar Dr. Abdullahi Ganduje.
A cikin wasikar, ya ce ya so ya cigaba da rike mukamin mataimakin gwamna har zuwa karshen wa’adin mulkin da aka zabe su, amma ya sauka ne saboda matsalolin da suka dabaibaye dangantakarsa da gwamnan jihar:
“Ina sanar da kai cewa na yanke shawarar sauka daga mukamin mataimakin gwamnan jihar Kano daga ranar Asabar 4 ga watan Agusta, 2018.

 

A cikin wasikar, ya kara da cewa, “Idan baka manta ba mai girma gwamna, na sha jan hankalinka ga wasu batutuwa da ka iya tada husumar da muke fuskanta a yau, amma kokarin nawa bai yi nasara ba.”
Kwamishinan watsa labarai na jihar Kano, Muhammad Garba, ya tabbatar da aukuwar wannan lamarin.
A wata hira da yayi da BBC, kwamishinan ya ce mataimakin gwamnan ya mika takardar barin aiki a fadar gwamnatin jihar Kano.
“Na bincika, kuma na tabbatar da cewa ya gabatar da wannan takarda a gidan gwamnati a yau din nan, kuma mun duba takardar da abin da ta kunsa.”
Kwamishinan ya kara da cewa, “Abin da yake nunawa shi ne cewa ya bar aiki a matsayinsa na mataimakin gwamnan jihar Kano.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *