Sabuwar Virus Din da Take sa Wayar Android Bindiga.

LATEST

Kasancewar kudin nan na zamani da ake kira da Cryptocurrency yayi tashin gwauran zabi wannnan yasa mutanen da suke tastarsa suke neman kowa ce hanya ta ganin na su ya karu dan samin gwaggwaban riba. menene cryptocurrency kuma ta yaya ake tastarsa wannan wata magana ce da zamu zo da ita nan da dan wani lokaci.

An samu shafikan yanar gizo da suke amfani da wayoyin mutane dan tastar wannan kudi ba tare da sanin su wadanda suke da wayarba. Ba iya yan kunar bakin wake ba wadanda aka fi kira da Hackers suke wannan mu’amala ba, har mutanen da suke da shafikan da yake sananne ma suna wannan harka kamar yadda shafin Adgaurd da yafitar da shafika kamarsu openload, Streamingo, Rapidvideo, da kuma onlinevideoConverter da suke kwace kwakwalwar wayar mutane dan tasu bukatar.

Ba’a tsaya anan ba kamfanin nan na birnin moscow dake kasar Russia yace akwai manhajoji na wayar android wadanda suke a matsayin tsaro ko kallan batsa amma ta bayan fage amfani suke da kwakwalwar wayar wajan tastar bitcoin ko wani kudin irin wannan. Ba iya tastar wannan kudi suke ba har kai harin nan na (DDoS) Distributor Denial of Service attacks.

Loapi, wata sabuwar manhaja da take aiki kala-kala a lokaci daya wajan aikin ta’addanci a lokaci wanda zai saka waya zafi kuma daga nan tai bindiga. Wannan manhaja a yadda aka tsara ta zata iya aikin tastar monero wadda yake daya daga cikin cryptocurrency ne ta dami wanda ya ake amfani da waya talla na bagaira ba dalili, kai harin DDoS, canja wa mai amfani da waya shafin yanar gizo da yake san ziyara zuwa wani daban, tura sako da kuma saka wasu manhajojin da ba’a so.Kamfanin na Kapersky sunce duk wayar da ta samu wannan matsala ta loapai bayan kwana biyu da samunsa, babbab abin tsoron shine wannan manhaja yar tada kayar tana yaki tukuru wajan kare kanta daga fita daga cikin wayoyin mutane kuma ana saminta a cikin manhajar wasu kamfaninkan da basu bayyana ba. Zamuyi amfani da wannan dama wajan kiran mutane dan kula da manhajojin da suke sakawa a wayarsu da kuma daga ina suke samo su. Dadin dadawa ma wajan kallo ko downloading bidiyo ana kula dank are waya daga bindiga.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *